Saturday, January 3
Shadow

Allah Sarki: Kalli Bidiyon yanda wannan Inyamurar Musulma ke kokawa da irin abinda Inyamurai Kiristoci ke mata

Wannan wata inyamura musulma ce da a dauki hankula a kafafen sadarwa saboda abinda tace Inyamurai Kiristoci na mata.

Ta bayana cewa, suna mata Bhàràzànà inda tace da tana kawar da kai ama abin sai karuwa yake.

Ta bayyana cewa tana a garin Nsukka ne kuma garinsu akwai zaman lafiya amma wasu na son kawo matsala.

Tace kiristanci bai koya abinda Kiristocin ke mata ba dan haka bata san inda suka samo irin abinda suke mata ba.

Tace kuma me ya shafesu da addinin da take yi?

Da yawa dai sun yi kira ga hukumomi da su dauki matakan da suka dace dan baiwa wannan matashiya kariya kada wani abu ya sameta.

Karanta Wannan  Ƙungiyar dattawan arewa ta buƙaci a yi bincike kan rikicin Natasha da Akpabio

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *