
Mawakin Najeriya, Burna Boy, Ya bayyana cewa yafi karfin Dala Miliyan $22.
Ya bayyana hakane yayin da ake hira dashi aka tambayeshi cewa, wai ana cewa dala Miliyan $22 ya mallaka a Duniya?
Sai yayi dariya yace ba zai fadi nawa ya mallaka ba amma a bar mutane su yi ta hasashe.
Da aka tambayeshi ko kudin nasa sun wuce haka? Yace sosai ma.