
Malamin Addinin Islama, Sheikh Lawal Triumph ya bayyana cewa Biliyan 1 ce aka baiwa Sheikh Khalifa Sani Zaria akan ayi tsafi dan a yi nasarar yiwa shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu juyin Mulki.
Yace dalili kenan da yasa aka kamashi.
Malam yace yasan da hakane ta hanyar kiran waya jihar Abinda ya faru, watau, Kaduna inda aka bashi wannan labari.
Duk da yake malam bai bayyana sunan malamin da yake nufi ba, da yawa sun fassara cewa, da malam Sheikh Khalifa Sani Zaria yake.
Yace irin wannan abinne ba za’a taba ganin dan Izala a ciki ba.