Saturday, January 10
Shadow

Kalli Bidiyon: Nifa gaba na daina zuwa coci, saboda na gano kawai Raina mana hankali ake>>Inji Wannan matar

Wannan wata matace data bayyana cewa, ta daina zuwa coci saboda ta gano gaba daya raina musu hankali ake yi.

Tace ta gaji da dukawa wasu turawa da aka saka musu hotunansu a coci ana cewa wai Jesus ne da mahaifiyarsa., Mary.

Tace karyane basu bane.

Tace Turawa da a yanzu da yawansu ma basu yadda da addini ba, yawancinsu abinda suka ga dama kawai suke aikatawa shine za’a ce sune Jesus da Mary?

Ta bayyana cewa, Mijinta ya rika ce mata wai shedan yayi galaba akanta.

Karanta Wannan  Watarana Talakawa Za Su Yi Kukan Rashin Shugaban ƙasa Bola Tinubu A Najeriya, inji fadar shugaban ƙasa

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *