
Tsohon Ministan sufuri, Rotimi Amaechi ya bayyana cewa, hanya daya da ADC zata kayar da APC a zaben 2027 shine ta tsayar da dan takarar shugaban kasa daga kudu.
Ya bayyana cewa, Karfin Tinubu a Kudu ne, idan aka samu dan takara daga kudu, zai raba kuri’ar kudun.
Dan haka sai a bar Arewa ta yanke shawarar wanda zai zama shugaban kasa.