
Dan wasan Barkwanci na Najeriya, Brother Shaggy da wata abokiyarsa da suke a filin wasan kasar Morocco yayin da Senegal ta dauki kofin AFCON, sun yi wani abu da ya dauki Hankula.
An gan su suna nuna bacin ransu bayan wasan alamar suna taya kasar Morocco Alhini.
Saidai a zahirin gaskiya suna jin dadi ne a ransu, Dalilin da yasa suke nuna Alhini a zahiri saboda suna zagaye da magoya bayan Morocco.
Lamarin ya dauki hankula sosai a kafafen sada zumunta