
Rahotanni sun karade kafafen sada zumunta cewa wai Gwamnatin Kano tace zata sauke me martaba sarkin Kano, Muhammad Sanusi II.
Wasu kuma na cewa Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf ya fara shirin sauke sarkin bayan komawarsa jam’iyyar APC.
Saidai duka wannan babu sahihancin labarin ko daya.
Abinda muka sani shine, Kwaishinan yada labarai, Ibrahim Waiya ya bayyana cewa, Gwamnatin na shirin kawo karshen rikicin masarautar ta Kano.
ya bayyana cewa, za’a dauki matakin sulhu da kuma tattaunawa da masu ruwa da tsaki a lamarin dan ganin an kawo karshen rikita-rikitar masarautar ta Kano.