
Rahotanni sun bayyana game da bukatun da Kwankwaso ya mikawa jam’iyyar APC kamin ya yadda ya koma jam’iyyar.
Saidai APC din ta ki amincewa da wadannan bukatu.
Rahotanni sun bayyana cewa Kwankwaso ya nemi a bashi iko da kaso 20 cikin 100 na jam’iyyar sannan a bashi kujerar mataimakin shugaban kasa.
Saidai APC din ta ki amincewa da hakanninda tace kujerar mataimakin shugaban kasa ba zaa baiwa kowa ba.
Rahoton yace dalili kenan da Kwankwaso yaki komawa APC din.
Allah ya kyauta yai mana mai kyau