
Matar nan ‘yar garin Daura da ake zargin ta kori mahaifiyarta daga gidanta sabida mahaifiyar ta kasa biyan kudin haya ta fito ta kare kanta.
Tace itama kamar yanda aka gani, haka taga lamarin a kafafen sada zumunta.
Tace mijin mahaifiyarta ne ke son sai ta sayar masa da gidan wanda gado ne da mahaifinta ya bar mata amma taki amincewa, tace tana tunanin yana da hannu game da abinda ke faruwa.
Wasu da a baya suka yi sharhi me kaushi akan matar sun fito sun bata hakuri.
Karanta Wannan Gwamnatin Jihar Katsina ta fitar da bayani kan yanda za'a gudanar da jana'izar Buhari