Wednesday, February 18
Shadow

Da Duminsa: Wani Babban Ma’aikacin Gwamnati ya je ya tsayawa Malam Nasiru Ahmad El-Rufai a bayar da belinsa saidai ya tsorata ya fasa

Rahotanni sun ce tsohon gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasiru Ahmad El-Rufai na ci gaba da zama a hannun EFCC a yayin da suke abincikensa kan zargin almundahanar Naira Biliyan 433 na jihar Kaduna.

Sahara Reporters ta ruwaito cewa da farko, EFCC sun bayar da sharadin cewa sai wani babban sakatare na Gwamnati ya tsayawa El-Rufai kamin su bayar da belinsa.

Saidai an samu wanda zai tsaya a bayar da belin nasa, amma da yaje sai EFCC suka ki amincewa dashi.

Daga baya ma ya janye daga maganar bayan da yayi zargin an masa Bqrqzqna.

Hakanan a yau, Laraba ne ya kamata tsohon gwamnan jihar Kadunan ya amsa gayyatar da ICPC suka masa kan wani zargin na daban.

Karanta Wannan  Ji abinda Mataimakin Gwamnan Kano, Comrade Aminu Abdussalam Gwarzo yayi kan komawar Abba Kabir Yusuf APC da ya jawo masa yabo

Saidai a yanzu da yake hannun EFCC babu tabbacin ko zai iya amsa gayyatar ta ICPC ko kuwa.?

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *