Sunday, September 27
Shadow

Kalli Bidiyon: Naji wasu ‘yan uwana ‘yan Kudu na tambayar shin wai da gaske akwai Hausawa a kasar Ingila? To akwai Hausawa a kasar Ingila kawai basu cika surutu bane kuma su basu dauke ta wata tsiyaba shiyasa basu babatu akai>>Inji ‘yar Najeriya Maryam Isha Olamide dake zaune a kasar Ingila

‘Yar Najeriya dake zaune a kasar Ingila, Maryam Isha Olamide tace wani dan uwanta dan kudu ya tambayeta wai akwai Hausawa dake zaune a kasar Ingila?

Ta bashi Amsar cewa Eh, akwai.

Ta gaya masa cewa, tana da abokai maza da mata dake zaune a kasar Ingila.

Tace kawai su basu cika surutu bane, yawancinsu karatu ke kaisu, kuma idan sun gama suna komawa gida Najeriya dan basu dauki Ingilar Aljannar Duniya ba.

https://www.tiktok.com/@maryama_ishaq/video/7609077332455869714?_r=1&_t=ZS-949dRTRiCSP

Karanta Wannan  ABIN TAUSAYI: Tun Yaron Yana Dan Watanni Hudu Da Haihuwa Suka Rabu Da Mahaifiyarsa, Hakan Ya Sa Bayan Girma Yake Fita Da Shi Aikin Achaba Saboda Babu Mai Kula Masa Da Shi

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *