
Sanata Saidu Muhammad Dansadau ya bayyana cewa, ba gaskiya bane zagin da akewa Janar TY Danjuma cewa bai son Musulmi.
Ya bayyana hakane a wajan wa’azin da yake a masallacin Apo Legislative Quarters.
Yace da yake sun yi Sanata tare da matar TY. Danjuma, ta rika bashi labarin cewa da zai samu gwamnan Zamfara da an magance matsalar tsaro.
Yace da ya fito takara sai matar TY Danjuma ta gaya masa cewa ga wanda yake bashi labari.
Yace Janar TY Danjuma ya aika masa Tallafin dala $500,000.