Akwai magunguna na gargajiya da yawa da ake amfani dasu dake ikirarin kara tsawon azzakari, saidai masana kiwon lafiya sun ce babu wani maganin dake kara tsawon Azzakari.
Masana kiwon lafiya sun ce hanya daya ce ake kara girman azzakari shine a yiwa mutum tiyata. Hakanan akwai wasu hanya kamar wata na’ura da ake bugawa azzakarin iska kaga ya mike, ko kuma na’ura me janyo azzakarin, saidai shima masana sunce wannan hanya bata cika yin aiki ba.
Saidai a lokacin da aka buga iskan, azzakarin zai iya mikewa sosai amma daga baya zai koma yanda yake, wasu suna samun karin girman azzakarin amma ba sosai ba yanda ake tsammani.
Saidai duka wadannan maganganu a kimiyyance muke magana, a gargajiyance da al’adu daban-daban mutane da yawa sun yadda zasu iya kara girman azzakarin su ta hanyar shan wasu magunguna ko shafawa akan azzakari.
Akwai kuma hanyar jan azzakari da hannu da ake yi wanda shima masana sun ce zai iya kara girman azzakari amma ba sosai ba.
Yanda ake yi shine ana kama kan azzakarin a daga sama a rika ja har na tsawon mintuna 10, ana iya yin hakan tsawon mintuna 10 sau 1 ko biyu a rana.