Sunday, March 15
Shadow

Tauraruwar mawakiyar Amurka, Nicki Minaj zata maka wani dan Najeriya a kotu saboda ya ce mata tsohuwa

Tauraruwar mawakiyar Amurka, Nicki Minaj ta bayyana shirin maka wani dan Najeriya a kotu saboda ya ce mata tsohuwa.

Nicki Minaj ta bayyana hakane bayan da mutumin me suna Dr. Penking ya bayyana ta a matsayin ‘yar shekaru 43 wadda kuma ta tsufa.

Inda ya kara da cewa ya kamata ta daina waka.

Saidai abin bai mata dadi ba

Da farko dai ta yiwa Lauyanta magana inda tace zasu saka dan Najeriyar cikin wanda zasu yi kararsu, saidai daga baya ko mi ta gani sai ta goge sakon.

Karanta Wannan  Kalli Bidiyon: Yanda aka kama wata Me ciki data Shàchì katan din Famfas

Saidai shi dan Najeriyar yace a shirye yake ya fuskanceta a kotu dan yana da ‘yancin fadar Albarkacin bakinsa kuma ra’ayinsa ya bayyana.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *