
Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya dawo gida Najeriya daga kasar Ingila inda yaje ziyarar aiki.
Shugaba Tinubu ya halarci Sallar Idi a jiya tare da mukarrabansa.
A sanarwar da ya fitar ta taya Musulmai barka da sallah, shugaba Tinubu ya godewa Allah da ya sa aka gama Watan Ramadana Lafiya.
Sannan ya jawo hankalin musulmai da su ci gaba da amfani da darasin da suka koya a wajan na Ramadana.
Shugaba Tinubu ya kuma jawo hankalin cewa aikin tsaro bana mutum daya bane, inda yace mutane su rika bayar da hadin kai wajan kai rahoton duk wani abu da basu gane masa ba.
Shugaban yace Shima kullun Allah yake roko ya kawo zaman lafiya, da ci gaba a Najeriya.