Wednesday, April 1
Shadow

Wata Sabuwa: An kama Direban Matar sarkin Kano da zargin satar Gwal na Naira Miliyan sittin

Rahotanni sun bayyana cewa, an gurfanar da direban matar me martaba Sarkin Kano, Muhammad Sanusi II da wasu mutane 2 a gaban kotun Magistrate dake Nomansland a Kano.

Ana zarginsu ne da satar Gwal na Naira Miliyan 60 da kuma karbar kayan sata.

Wadanda ake zargin sune Sulaiman Yakubu Kulkude, Idris Musa, da Abdullahi Usaini.

Hakanan ana zarginsu da satar kudi da kuma wayar hannu.

Yayin zaman kotun, Sulaiman ya amsa duka laifukan da akw zarginsu da aikatawa saidai sauran biyun da ake zargi sun musanta zargin da ake musu.

Lauyan wadanda ake zargin, Barrister A.A. Abdullahi ya bukaci a bashi belin wadanda ake zargin inda mai shari’a, Magistrate Halilu Abdurahman ya bayar da belin da sharuda masu tsanani.

Karanta Wannan  Allah Sarki: Kalli Bidiyon yanda rasuwar Fulani ta taba Tauraron fina-finan Hausa, Tijjani Asase sosai ya fashe da kuka

Yace dole duk wanda zai karbi belinsu ya zamana ma’aikacin Gwamnati dake mataki na 15 sannan dole ya ajiye kudin beli na Naira Miliyan 10.

Sannan ya daga ci gaba da sauraren karar har sai nan da 14 ga watan Afrilu inda yace a kai wadanda ake zargin gidan yari har sai sun cika sharudan belin da aka bayar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *