
Bayan kaddamar da gidauniyar neman tallafin ciyar da talakawa da matar shugaban kasa, Remi Tinubu ta yi a ranar Alhamis.
Gwamnoni da Dangote da sauran ‘yan kasuwa sun tara mata Naira Biliyan 66.
Ministan lafiya da walwala, Prof Ali Pate ne ya tabbatar da hakan a jawabin da yayi.
Rahoton yace Dangote ya bayar da tallafin Naira Biliyan 20.
Kamfanin mai na kasa, NNPCL sun bayar da tallafin Naira Biliyan 10
Wasu abokan matar shugaban kasar sun bayar da tallafin Naira $500,000. Gidauniyar The Emeka Offor Foundation ta bayar da tallafin Naira Miliyan 500.
Yace hakanan shugaba Tinubu ya amince a fitar da Naira Biliyan 17 dan wannan aiki.
Sannan kowace jihar Najeriya ana tsammanin ta bayar da tallafin Naira Miliyan 500 wanda idan jihohi 36 suka bayar, Za’a tashi da Naira Biliyan 18 kenan.