Friday, April 3
Shadow

Da Duminsa: Fadar shugabab kasa ta bayyana dalilin da yasa shugaba Tinubu bai shiga cikin garin Jos ba ya tsaya a filin jirgi, a ziyarar da ya kai jiya

A jiyane dai shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya kai ziyara garin Jos na jihar Filato saidai hai shiga cikin gari ba a filin jirgi ya tsaya aka kai masa iyalan wadanda lamarin ya rutsa dasu ya gana dasu.

Tsohon Mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar na daga cikin ‘yan Najeriya da suka yi Allah wadai da wannan mataki inda suka ce hakan nun rashin kulawa ne.

Saidai da yake jawabi kan lamarin, me magana da yawun shugaban kasa, Bayo Onanuga ya bayyana cewa, Shugaba Tinubu bai shiga cikin garin Jos bane saboda Titin jirgin saman na da matsala, idan dare yayi ba’a iya amfani dashi.

Karanta Wannan  Kotu Ta ce a daura auren Maiwushirya da 'yarGuda nan da kwanaki 60

Yace kuma daga Filin jirgin zuwa wajan da ya kamata Tinubu ya je a cikin gari tafiyar mintuna 40 ne kamin ya je ya dawo duhu yayi shiyasa kawai aka yi shawarar ayi taron a filin jirgin saman.

Hakanan yace dalilin da yasa shugaba Tinubu ke gaggawa a jiyan, akwai ganawar da zai yi da shugaban kasar Chadi data shafi harkar tsaron kasashen Biyu.

Yace kuma shugaba Tinubu ya gayyaci shuwagabannin Al’umma na Jos zuwa Abuja dan tattauna yanda za’a shawo kan matsalar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *