Thursday, January 2
Shadow

Yadda ake lemun kwakwa

Abubuwan da ake bukada dan hada lemun kwakwa:

Kwakwa Kwallo daya:

Madarar Ruwa gwagwani daya

Madarar Gari kofi daya.

Suga babban cokali 5.

Citta Kwaya daya, danya ba busassa ba.

Kanunfari kwaya 6

Kankarar ruwa me sanyi.

Yanda za’a hada:

A fasa kwakwar a juye ruwa a kofi ko mazubu me kyau, a cire bawon kwakwar a yayyankata kananan-kanana. A zuba a blender a zuba ruwan kwakar a ciki a markada.

Idan ba’a da blender ana iya yin amfani da turmi ko a kai markade.

A zuba cittar da Kanunfarin da aka tanada.

A zuba sukarin da aka tanada.

A zuba masarar garin da aka tanada.

A markade ko a yi blending ko a daka har sai yayi sosai duk sun hade. Sai a tace.

Karanta Wannan  Gyaran fuska da man kwakwa

A zuba madarar ruwan da aka tanada.

Idan ana so ana iya kara sukari.

Sai a saka kankara me sanyi wadda aka tanada.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *