Friday, April 24
Shadow

Allah Sarki Kalli Bidiyon hirar tsohon dan wasan Arsenal, Emmanuel Eboue wanda ya auri baturiya, saidai yanzu yace ta rabashi da ‘ya’yanshi sannan ta kwace duka kadarorin da ya mallaka

Tsohon dan wasan Arsenal, Emmanuel Eboue ya koka da maganar hanashi mu’amala da ‘ya’yansa da matarsa ta yi.

Matarsa dai ‘yar kasar Belgium ce kuma a lokacin da yake ganiyarsa ya aureta, saboda rashin Ilimi ya mika mata ragamar komai na kudinsa.

Saidai ta yi amfani da wannan dama wajan arzuta kanta ta mallakawa kanta duka kadarorinsa har kotu aka shiga amma ita tayi nasara sannan kotu ta bata damar kula da ‘ya’yansu.

Yace a yanzu ta hanashi ganawa da ‘ya’yan nashi kuma yana da lambarsu, zai aika musu da sako amma ba zasu aika masa da amsa ba.

Karanta Wannan  Da Duminsa: A karin Farko Musulmi ya zama magajin garin New York City, na kasar Amurka

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *