
Tsohon dan wasan Arsenal, Emmanuel Eboue ya koka da maganar hanashi mu’amala da ‘ya’yansa da matarsa ta yi.
Matarsa dai ‘yar kasar Belgium ce kuma a lokacin da yake ganiyarsa ya aureta, saboda rashin Ilimi ya mika mata ragamar komai na kudinsa.
Saidai ta yi amfani da wannan dama wajan arzuta kanta ta mallakawa kanta duka kadarorinsa har kotu aka shiga amma ita tayi nasara sannan kotu ta bata damar kula da ‘ya’yansu.
Yace a yanzu ta hanashi ganawa da ‘ya’yan nashi kuma yana da lambarsu, zai aika musu da sako amma ba zasu aika masa da amsa ba.