
A wani Bidiyo da ya watsu a kafafen sada zumunta, an ga shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu an masa wankan tsarki irin na Kiristoci sannan aka rataya masa Kross.
Lamarin ya baiwa mutane mamaki kasancewar kowa yasan Tinubu musulmi ne.
Dino Melaye na daga cikin wadanda suka bayyana mamakinsu game da lamarin inda yace shin ko shugaban kasar ya raba kafane?