
Fatima Naseer Teemahcool wadda itace shugaban Gida-Gida na Tiktok wadda kuma itace ta jagoranci daga jan dan kamfai a Kano wanda suka sakawa sunan dan kamfan tsula ta samu mukamin siyasa.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa, shugaban karamar hukumar Nasarawa, Yusuf Imam Ogan Boye ne ya bata shugabar harkokin mata na karamar Hukumar.
Rahoton yace a yau, Alhamis ne takardar bata mukamin ta fito.
Ta dai fito ta bayar da hakuri kan daga dan kamfai din data yi inda tace ba zata sake aikatawa ba