
Hukumomi a Kano sun kama wani mutum me suna Mohammed Saidu saboda tara kashin mutane buhu-buhu a kofar gidansa.
Hakan yasa wari ya damu mutanen unguwar inda aka yi ta kokarin yin magana dashi dan ya daina amma yaki.
Hakane yasa makwabtansa suka kai maganar zuwa kotu.
Mai Shari’a Halima Wali ta kotun Magistrate ta yanke masa hukuncin daurin kwanaki 14 a gidan yari da kuma tarar Naira 100,000.
A yayin zaman kotun dai Muhammad Saidu wanda sana’ar kwashe kashi yake yace yana tarawa ne yana sayarwa da manoma inda ya amsa zargin da ake masa.
Kotu ta bashi umarnin dauke kashin daga kofar gidansa sannan yayi alkawarin ba zai sake tarawa ba.