Thursday, July 16
Shadow

Tinubu ya gaya mana cewa ba zai goyi bayan zaben gaskiya ba, wanda ya ga dama yayi zabe wanda bai ga dama ba kar yayi>>Inji Dan takarar jam’iyyar SDP Adewole Adebayo

Dan takarar shugaban jam’iyyar SDP, Adewole Adebayo ya zargi shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu da cewa yace ba zai goyi bayan zaben gaskiya ba.

Adewole yace sun je sun samu shugaban kasar ne kan yanda za’a gyara harkar zabe amma ya gaya musu cewa shima lokacin yana da adawa ya sha wuya sannan kuma zabe iyawane, wanda ya iya Allonsa ya wanke.

Ya bayyana cewa, shugaban kasar ya gaya musu cewa suna bata masa rai.

Adewole yace a daidai wannan lokacin ya daina kallon Tinubu a matsayin shugaban kasa inda yake kallonsa kamar kowane dan siyasa.

Karanta Wannan  Yawan wanda suka kasa biyan bashin da suka ci a bankunan Najeriya sun karu

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *