Sunday, June 28
Shadow

Kalli Bidiyon: Gwamnan jihar Kaduna, Malam Uba Sani ya kai ziyara gidan malamar da aka zarga da satar yara inda ya sha Alwashin kula da yaran data bari kamar nasa

Gwamnan jihar Kaduna, Malam Uba Sani ya bayyana cewa, zai dauki nauyin ‘ya’yan matarnan da aka yiwa kazafin satar yara a Maraban Jos Kaduna kamar ‘ya’yansa.

Ya bayyana hakane a yayin ziyarar ta’aziyya da jaje da ya kaiwa iyalan mamaciyar.

Sannan yace an kama mutane 100 da hannu a lamarin inda yace guda 40 suna da hannu kai tsaye a lamarin sannan akwai sauran da ake zargi da yin gangamu ba bisa ka’ida ba.

Yace zasu tabbatar an musu hukuncin da ya dace dan kada gobe ma wasu su kara.

@jkdmedia_

Gwamnan jihar Kaduna Sanata Uba Sani yace an kama mutane 41 da hannu dumu dumu wurin kisar Malamar Islamiyyar nan da aka yiwa kisan gilla a maraban jos a kaduna. Reporter: Abubakar Yakubu Margi 📸 Hussaini Aminu Muhammad

♬ original sound – JKD TV/Hamada FM
Karanta Wannan  Kalli Bidiyon yanda ta kaya bayan da wata mata ta kama Mijinta da Budurwarsa a Otal

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *