
Gwamnan jihar Kaduna, Malam Uba Sani ya bayyana cewa, zai dauki nauyin ‘ya’yan matarnan da aka yiwa kazafin satar yara a Maraban Jos Kaduna kamar ‘ya’yansa.
Ya bayyana hakane a yayin ziyarar ta’aziyya da jaje da ya kaiwa iyalan mamaciyar.
Sannan yace an kama mutane 100 da hannu a lamarin inda yace guda 40 suna da hannu kai tsaye a lamarin sannan akwai sauran da ake zargi da yin gangamu ba bisa ka’ida ba.
Yace zasu tabbatar an musu hukuncin da ya dace dan kada gobe ma wasu su kara.