Tuesday, July 21
Shadow

A karin Farko, Budurwar Tsohon shugaban kasa, Marigayi Janar Sani Abacha da ya rasu suna tare ta bayyan ainahin abinda ya faru

A cikin wani littafi da tsohon jami’in hukumar DSS me suna Dennis Amachree ya rubuta, ya bayyana cewa, shine ya binciki Budurwar tsohon shugaban kasa, Marigayi, Janar Sani Abacha wadda suna tare ne tsohon shugaban ya rasu.

Amachree yace Janar Sani Abacha ya rasu ne a cikin fadar shugaban kasa yayin da suke tare da Budurwarsa a dakin saukar baki na cikin fadar.

Yace da budurwar Abacha ta lura da ya rasu sai ta tsere ta hau jirgi ta tafi Legas.

Yace amma sun bibiyeta suka kamota.

Yace da suka kamota ta bayyana musu cewa, ba ita ta Qashe Abacha ba, suna tsaka da soyayya akan gado ya rasu.

Karanta Wannan  Bamu so Abinda ya faru tsakanin Kwankwaso da Ganduje ya faru da Abba>>Inji Tijjani Gandu

Yace bayan ya kammala Bincike ta ne sai aka mayar da ita zuwa Abuja.

Yace wannan shine ainahin abinda ya faru sabanin abinda aka ruwaito a kafafen watsa labarau.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *