
Rahotanni sun bayyana cewa, Gwamnatin tarayya ta kaddamar da shirin YOUTHCRED ranar Laraba wanda shiri ne na samarwa matasa da bashi ko tallafi dan fara sana’a ko karfafa wadda suke yi.
Ministan Kudi, Taiwo Oyedele, ya tabbatar da hakan inda yace matasa 500,000 ne ake tsammanin zasu amfana da bashin.
Yace kuma za’a baiwa kowane matashi daga Naira Dubu dari biyu zuwa Naira Miliyan biyu.
Yace an kawo bashinne dan saukakawa matasa samun bashi maimakon yanda bankuna ke bukatar sai an basu jingina kamin su bayar da bashi.
Yace matasa daga shekaru 18 zuwa 35 zasu iya neman bashin.
Yace dolene mutum ya nuna shaidar kudin shiga da yakw samu sannan ya nuna aniyar son biyan bashin idan an bashi.
Yace mutum zai iya bayyana yaushe yake son biyan bashin? Daga wata 1 zuwa watanni 12.
Sannan yace ba’a bukatar jingina ko wani ya tsaya maka, abinda kawai ake bukata shine mutum ya nuna yawan kudin da yake samu wanda da wannan za’a yi la’akari wajan amincewa da bashin da za’a bashi.
Yace masu sana’o’i n hannu irin su dinki, gashin kek, da cincin da sauransu, manoma, Kanukawa da sauransu duk zasu iya neman bashin.