
Fadar Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ta mayar da martani kan rahoton cewa, Atiku Abubakar ya kaiwa shugaban kasar Amirka, Donald Trump tsegumin cewa ana zargin Shugaba Tinubu da safarar Qaya.
A sanarwar da ya fitar ta bakin me magana da yawunsa, Bayo Onanuga, Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu yace Atikun ya kamata a sanshi da kima da kamun kai da sanin ya kamata
Yace amma duk ya zubar da wannan ya koma yin abubuwan kananan mutane na zubar da girma.
Yace Tuni kotu ta wankeshi akan maganar zargin safarar qaya.
Yace kamata yayi Atiku ya kawo tsare-tsaren da zai yi amfani dasu dan gyara Najeriya wanda hakan zai ja hankalin ‘yan kasa su zabeshi amma ba bata suna ba.
Yace Shi abinda Atikun yayi ko a jikinsa.
Yace amma fa shima Atikun da a kasar China yake da tuni an dade da Shekyeshi saboda sata.
Yace Atikun fa shima yana da kashi a gindi a kasar Amirkar inda shima an taba wata shari’a ta rashawa da cin hanci wadda ta shafeshi shi da matarsa.