Friday, July 24
Shadow

Maimakon ka kama Girmanka ka zabi yin abin kana nan mutane da bata min suna>>Shugaba Tinubu ya gayawa Atiku bayan da Atikun ya kaiwa Shugaban Amurka tsokacin zargin Tinubu da safarar Qaya

Fadar Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ta mayar da martani kan rahoton cewa, Atiku Abubakar ya kaiwa shugaban kasar Amirka, Donald Trump tsegumin cewa ana zargin Shugaba Tinubu da safarar Qaya.

A sanarwar da ya fitar ta bakin me magana da yawunsa, Bayo Onanuga, Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu yace Atikun ya kamata a sanshi da kima da kamun kai da sanin ya kamata

Yace amma duk ya zubar da wannan ya koma yin abubuwan kananan mutane na zubar da girma.

Yace Tuni kotu ta wankeshi akan maganar zargin safarar qaya.

Yace kamata yayi Atiku ya kawo tsare-tsaren da zai yi amfani dasu dan gyara Najeriya wanda hakan zai ja hankalin ‘yan kasa su zabeshi amma ba bata suna ba.

Karanta Wannan  Kalli Bidiyo Da Duminsa: Mummunan Hadarin Motar da ya sameni jiya, Jiface ta aka yi min kawai dan na bayar da kyautar Dalar Amurka 100, amma Addu'ar iyaye na ce ta kareni>>Inji Tauraruwar Kannywood, Samha M. Inuwa

Yace Shi abinda Atikun yayi ko a jikinsa.

Yace amma fa shima Atikun da a kasar China yake da tuni an dade da Shekyeshi saboda sata.

Yace Atikun fa shima yana da kashi a gindi a kasar Amirkar inda shima an taba wata shari’a ta rashawa da cin hanci wadda ta shafeshi shi da matarsa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *