Friday, July 24
Shadow

Tonon silili: Na rantawa Gwamnan Kaduna, Uba Sani Naira Miliyan 30 yayi yakin neman zabe da alkawarin zai mayar da Naira Miliyan 100 idan ya zama gwamna amma yanzu ya hanani kudina>>Inji Ummi El-Rufai (TUGE)

Daya daga cikin yaran tsohon gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasiru Ahmad El-Rufai me suna Ummi El-Rufai TUGE ta zargi gwamnan jihar Kaduna, Malam Uba Sani da kin biyanta bashin Naira Miliyan 30.

Tace Ta ranta masa Naira Miliyan 30 yayi yakin neman zabe da alkawarin cewa idan ya zama Gwamna zai mayar mata da riba kudin su zama Naira Miliyan 100 amma yanzu yaki biyanta.

Tace ita a yanzu ma ba wai ribar take nema ba, tana neman kudinta su fito ne watau Miliyan 30 din.

Tace A wancan lokacin da suka yi yakin nema zabe kowa ya sani babu kudi ana Cashless inda tace dalili kenan da Uba Sani ya roketa ta bashi rancan wadancan kudin.

Karanta Wannan  Ko a Mafarki ban taba Tunin za'a janye min 'yansandan dake bani tsaro ba>>Sanata Ningi

Tace duk da dai itama tasan son banza ne ya kaita amma dai ya biyata hakkinta, ta bayyana hakane a shafinta na Tiktok a wani dogon Bidiyon data wallafa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *