Monday, December 16
Shadow

Maganin farin ruwa mai karni

Ruwan dake fita daga gaban mace ba matsala bane, kuma ba zaki iya dakatar dashi ba domin haka jikinki yake, Haka Allah ya halicceshi.

Fitar ruwan na faruwa ne dan wanke al’aurarki da kasancewarta cikin koshin lafiya.

Saidai yakan iya zama alamar cuta idan ya zama ruwan yana:

Saki jin kaikai.

Yana da wari ko karni kamar na kifi.

Yayi kalar toka ba mai duhu ba ko ace kalar mugunya.

Yana fita da gudaji-gudaji.

Yana sa ki ji zafi yayin fitsari

Ya canja kala zuwa green ko ruwan ganye.

Dalilin da yasa kike ganin farin ruwa me karni a gabanki.

Likitoci basu kai ga sanin duka abubuwan dake kawo irin wannan ruwa me karni da yauki a gaban mace ba ko ace infectio ba, amma akwai abubuwan da ke taimakawa wajan kamuwa da infection da aka fi sani kamar haka:

Karanta Wannan  Gyaran jiki bayan gama al'ada

Yin Jima’i ba tare da amfani da kwandom ba ko kuma yin jima’i da mutane da yawa.

Ciwon sugar wanda ba’a kula dashi.

Shan maganin hana daukar ciki.

Cutar Kanjamau ko idan garkuwar jikin mutum ta yi rauni.

Amfani da sabulu, mai ko turare a gaban mace wanda jiki baya so yana yin reaction.

Tura wani abu cikin al’aura.

Maganin farin ruwa me karni

Ana iya maganin farin ruwa me karni da Yoghurt wanda bai da sugar.

Eh kin jini da kyau, Yoghurt dai ko ince Yegot, fari wanda ake sha. Amma kada a sake a yi amfani da me sugar ko sikari,a yi amfani da wanda bashi da sugar.

Karanta Wannan  Amfanin man ridi a gaban mace

Bincike daban-daban na masana kiwon lafiya ya tabbatar da amfanin Yegot wanda bashi da sugar wajan maganin ciwon sanyi ko farin ruwa me karni a gaban mace.

Ana iya shan yegot din shi kadai,zai iya bayar da abinda ake bukata, hakanan kuma ana iya shafashi akan gaban mace sannan a tura wani ciki.

Hakanan kuma ana iya hada yegot din wanda bashi da sugar da zuma a kwaba, a rika amfani dashi kamar ma shafawa a gaban mace.

Amfani da man kwakwa

Ana iya amfani da man kwakwa wajan kawar da matsalar farin ruwa me karni, yana magani sosai, saidai a tabbatar an samu man kwakwa na gaskiya wanda ba’a mai hadi da komai ba.

Karanta Wannan  Ya ake gane mace ta balaga

Ana kuma iya amfani da tafarnuwa wajan magance matsar farin ruwa me karni, kawai a rika amfani da tafarnuwa a cikin abinci amma kada a rika turata a cikin farji ko gaban mace.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *