Monday, July 27
Shadow

Kalli Bidiyon: Sultan Abdulrazaq ya bayyana irin cin amanar da Momi Gombe da Bilkisu Shema suka masa

Tauraron kuma me shirya fina-finan Hausa, Sultan Abdulrazaq ya bayyana irin cin amanar da Momi Gombe ta masa.

Ya bayyana cewa, shine ya farawa Momi Gombe fim din da aka santa sosai ya shahara a Duniya sannan ya mata fina-finan daban-daban.

Yace amma kwatsam suna cikin aiki sai ta tsere ta ki dawowa su ci gaba kuma gashi itace jaruma a fim din.

Yace ya mata kiran Duniya amma taki daga masa waya, yace haka ya hakura da fim fin bayan narka kudade yayi asara.

Yace a karo Na biyu Momi Gombe ta sake masa haka.

Yace bayan Momi Gombe Itama Bilkisu Shema na shirin yi masa irin hakan.

Karanta Wannan  Ku yi hankali,Masu ikirarin Jìhàdì na son mamaye kasarku>>Kasar Amurka ta gargadi Najeriya

Ya kara da cewa, abinda ke faruwa shine da mutane sun lura ka fara fim da jaruma fim ya samu daukaka sai a zuga jarumar ace ta bijire maka.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *