Tuesday, August 11
Shadow

Khadija Muhammad na ƙoƙarin tona asirin wani a Kannywood — amma ta ƙi bayyana sunansa!

Jarumar Kannywood Khadija Muhammad ta bayyana cewa tana ƙoƙarin tona asirin wani mutum a Kannywood da take zargin ya ƙi biyan ta hakkinta.
Abin da ya ƙara ɗaukar hankalin mutane shi ne yadda ta yi wasu bayanai da suka sa mutane ke ƙoƙarin gano wanda take magana a kansa. Wasu ma sun ƙagu ta saka hotonsa ko ta ambaci sunansa, amma har yanzu Khadija ba ta bayyana sunan mutumin ba.

Sai dai a cikin bayaninta, ta yi masa wata siffa mai ban dariya, inda ta ce “shi ya sa yake da ƙaton tumbi, ashe duk haƙƙinmu a ciki yake.”

Ku a ganinku, ya kamata Khadija ta bayyana sunan mutumin da take zargi, ko ta nemi hakkinta ta hanyar da ta dace ba tare da tona sunansa a kafafen sada zumunta ba?

Karanta Wannan  Bidiyo: Wannan Mutumin yace wai an masa Wahayin ya kera jirgin ruwa saboda ranar Kirsimeti Duniya zata tashi

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *