
Kungiyar taurarin fina-finan Hausa me suna Kannywood Media forum ta fita zanga-zanga inda take kira ga ‘yan arewa kada su sake zaben shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu a zaben 2027.
Tahir Fagge da sauran wasu jarumai ne suka jagoranci zanga-zangar inda aka ji suna cewa kada a zabi shugaban kasar a zabe me zuwa.