Saturday, September 12
Shadow

Ana zargin daya daga cikin yaran Farfesa Isa Ali Pantami da wallafa cewa idan me gidansu ya ci zabe zai hana Maulidi a jihar Gombe

Ana zargin Daya daga cikin manyan yaran dan takarar Gwamnan jihar Gombe, Farfesa Sheikh Isa Ali Pantami, watau Abba Pantami da yin wallafa a shafinsa na sada zumunta inda ya rubuta cewa, Idan Pantami ya ci zaben gwamnan jihar Gombe zai hana Maulidi.

Screenshot na rubutun nasa yana ta yawo a kafafen sada zumunta inda ake ta sharhi akai.

Inda a shafin Tauraron fina-finan Hausa Baba Sadiq aka fara ganin screenshot din wanda daga baya ya ci gaba da yaduwa.

Zuwa yanzu dai Abba Pantami bai ce komai kan lamarin ba.

Karanta Wannan  A lokacin tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan an min tayin Naira Miliyan 80 in tallatashi amma naki yadda>>Inji Ali Jita

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *