
Matashi ya zo da sauri ya kama sahun gaba ta yadda ba zai yi nesa da liman ba sosai, bayan an idar da sallah sai Sheikh Lukuwa Sokoto ya juyo ya fuskanci mutanen cikin masallaci sai aka fara zuwa ana gaisawa da shi, caraf sai matashin nan ya je kusa da malam don su gaisa, nan ne ya samu damar yiwa malam abinda bai kamata ba InnaliLLAH wa’inna ilaihi rajiun!
Cikin ikon Allah hanzarin da mutane suka yi wajan kaiwa malam dauki yasa matashin bai yi nasarar abinda yaje aikatawa ba, sai mutane suka kawo ɗauki aka kama shi kuma aka yi nasarar aika matashin lahira.
Wannan shi ne abin da ya faru, muna fata wannan zai zama izina ga sauran malamai da limamai sannan ƴan agaji da masu tsaron malamai da limamai su ma su zama masu lura da irin wannan salo.
Sannan rahoto ya zo cewa sauran masu irin wannan hali sun fara tuba kuma suna guduwa suna barin jihar Sokoto, wasu kuma sun ɓuya a cikin lungunan jihar ta Sokoto kamar yadda shi ma babban mai da’awar wato Mai-barewa shi ma yana gidan-yàri a ɗaure. Alhamdu LILLAH.
Allah ƙara tsare malaman sunnah, Allah ya shiryi ƴan bidi’ar Sokoto da Najeriya bakiɗaya su tuba zuwa ga sunnah.
Alƙalin bayan fage,
Ahmad Usman Elnafaty.
Tuni dai jami’an tsaro suka ke suka dauke gawar matashin
A jiyan, An garzaya da Sheikh Musa Lukuwa asibiti amma cikin ikon Allah bai jima ba aka sallameshi
Sannan Sheikh Musa Lukuwa ya fito yace yana cikin koshin lafiya mutane su kwantar da hankulansu.