
Wasu ‘yan Najeriya dake kasar Saudiyya, sun yiwa Matashin da ya kutsa masallacin Sheikh Musa Lukuwa a Sokoto Salatil Ga’ib.
An gansu suna sallar a Saudiyya inda wasu ke jinjina musu.
Bayan faruwar lamarin dai an garzaya da Sheikh Musa Lukuwa Asibiti inda daga baya aka sallameshi bayan da ya samu kulawar gaggawa kuma yace yana nan a raye.
Hakanan sabbin Rahotannin da muke samu na cewa, hukumomi a jihar Sokoto, sun kulle masallacin Sheikh Musa Lukuwa.