Thursday, September 24
Shadow

Kalli Bidiyon: Kotu ta fara kwace kadarorin Rahamaniyya saboda samunsa da laifin cinye kudin da wasu turawa suka bashi ya kai musu man fetur

Rahotanni sun bayyana cewa, Kotu ta fara kwace Kadarorin shahararren dan kasuwa, Alhaji Abdulrahman Musa Hassan shugaban kamfanin Rahamaniyya Group bayan samunsa da laifin cinye kudin kaiwa turawa man fetur da suka bashi.

Turawan dake da kamfanin Petrichor Energy FZCO and Ultimate Oil & Gas sun baiwa Rahamaniyya dala Miliyan dari hudu, $400M ya kai musu man jirgin sama da Gas amma bai kai musu ba a shekarar 2022 zuwa 2023.

Wannan ne yasa suka makamashi a kotu a kasar Ingila inda kotun ta yi hukuncin cewa a kwace duka kadarorinsa dake fadin Duniya dan a biya kudin da yaci.

Kotun ta ingila ta aikowa da Najeriya wannan umarni inda tuni aka fara aiwatar dashi aka fara kwacw kadarorinsa kamar yanda zaku gani a kasa.

Karanta Wannan  Da Duminsu: Shugaban kasar Amurka Donald Trump zai haramtawa 'yan Najeriya shiga Amurka

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *