
Me martaba sarkin Katsina, Abdulmumin Kabir Usman na ta shan Yabo saboda yanda ya tsagewa Kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu da suka kai masa ziyara Gaskiya.
A cikin wani Bidiyo dake ta yawo a kafafen sada zumunta an ji Sarki na ce musu kada su yi karyar abinda suka san ba zasu iya yi ba.
Sannan ya koka musu kan matsalar tsaro a yankin Arewa maso yamma inda yace an hana mutane Noma.
Hakanan yace An kulle kamfanoni da yawa a Arewa.