Friday, October 23
Shadow

An girke ‘yanda a wajajen da aka lika fastocin yakin neman zaben Shugaba Tinubu saboda kada matasa su yaga fastocin

Rahotanni daga jihar Kaduna na cewa, An girke jami’an ‘yansanda a duk guraren da aka kafa fastocin yakin neman zaben shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu a fadin jihar dan su hana matasa yaga Fastocin.

Wani daga cikin ‘yansandan da aka baiwa aikin tsare fastar shugaban kasar yace an ajiye sune a kan babbar hanyar da shugaba Tinubu zai bi idan ya je Kaduna.

Yace kuma da dare suka fi yin aiki saboda a lokacinne ake sa ran matasa ka iya zuwa su lalata fastocin.

Hakan na zuwane a yayin da shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu zai je Kaduna ranar Asabar dan kaddamar da yakin neman zabensa na 2027.

Karanta Wannan  Saika fice mana daga jam'iyya tun da ka shiga gayyar su Atiku>>Labour Party ga Peter Obi

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *