A karshe dai, kasashen Tarayyar Turai karkashin EU sun juyawa kasar Israela baya.
Kasashen sun fito sun nemi a kakabawa kasar Israela takunkumi saboda kisan kiyashin da takewa Falas-dinawa.
Hakan ya biyo bayan nacewa da kasar ta yi cewa sai ta shiga Rafah inda dubban fararen hula na Falasdinawa ke gudun Hijira.
Kasar kuma ta kai wani mummunan hari a sansanin ‘yan gudun hijirar wanda ya kone mutane akalla 50 kurmus ciki hadda yara kanana.
Lamarin ya jawowa kasar Israela Allah wadai wanda daga baya Firaministan kasar, Benjamin Netanyahu ya fito yace kuskurene kuma suna bincike akai.