Matar Shugaban kasa,Remi Tinubu ta kashe Naira Miliyan 701 a zagayen da ta yi a kasashen Duniya guda 5.
Ko da a shekarar 2023 sai da fadar shugaban kasa ta warewa ofishin matar shugaban kasar Naira Biliyan 1.5 dan saya mata motoci na Alfarma.
An gano hakanne a kundin tattara bayanai na gwamnatin tarayya na yanar gizo.
Bayan wannan kuma, Gwamnatin ta kashewa Matar shugaban kasar Naira Miliyan 314 wajan shirya taruka a cikin gida Najeriya.