Friday, December 12
Shadow

Rikicin Aminu J Twon, Ordinary President da matar soja, Waye me gaskiya?

Matar soja Seaman Haruna Abbas ta dauki zafi sosai akan neman taimakon da Aminu J. Town yace ya mata inda ta yi ikirarin cewa ba da saninta bane.

Hakanan Shima Ordinary President, Ahmad Isah wanda ta je gidan talabijin da rediyonsa wajan neman hakkin mijinta, ya dauki zafi duk da dai yawa Aminu J. Town Nasiha.

Hakanan a bangaren Aminu J. Town, shima bai dauki abin da sauki ba inda yayi zargin cewa ana son bata masa suna.

Aminu J. Town dai ya bayyana cewa an nemi ya tarawa matar sojan ruwa, Seaman Haruna Abbas wadda ta kai kara gidan talabijin na Ordinary president inda tace an tsareshi tsawon shekaru 6 ba tare da hukunci ba kan zargin yayi yunkurin kashe ogansa.

Karanta Wannan  Mun bar gidan kakan mu ba gyarane saboda bamu saci kudi ba, ba zamu iya kula da gidan ba>>Inji Jikan Tsohon Shugaban kasa, Alhaji Shehu Shagari

J Town yace yayi kokarin neman lambar matar inda ya kira dan neman izinin tara mata taimakon.

Ga bidiyon wayar da Ordinary president yayi da Aminu J. Town:

@refresh0022

Pls say something positive on this two people bcus of the good work and helpful may Allah grant them jannahamaminujtownrbreketefamilyo#foryou

♬ original sound – Bin Usman

Saidai daga baya matar tace da wayarta yayi amfani amma ba da ita yayi magana ba, J. Town ya nemi ta gaya masa da wa yayi magana amma matar tace ba zata fada ba.

https://www.tiktok.com/@dan_gaya2/video/7415365371621854470?_t=8pqeaheDtEE&_r=1

Hakan ya batawa J. Town rai inda ya zargi Ordinary president, Ahmad Isa da yin wata kullalliya akan lamarin.

Karanta Wannan  Wata Sabuwa: Ana shirya zanga-zanga nan da 1 ga watan Augusta saboda rashin abinci, rashin aiki, rashin tabbas a rayuwar matasan Najeriya

Lamarin dai tsakanin mutanen 3 ya rincabe inda Matar tace da wayarta J Town yayi magana amma ba ita ta yi magana dashi ba akan ya nema mata taimako ba kuma ba zata fadi wadda ta yi magana da J. Town din ba

A karshe dai an ga matar tana tofin Allah tsine ga J. Town bisa zargin yayi amfani da sunanta ya tara kudi inda kuma takewa Fauziyya D. Sulaiman ta Arewa24 godiya.

Wasu rahotanni sun bayyana cewa, Fauziyya D. Sulaiman ta tarawa matar sojan ruwan Naira Miliyan 2.1 kuma Ordinary president ya amince da wannan tallafin kudi.

@moh___zyynsanee

Moh_Zyynsanee • 9,4 Moh_ Zyynsanee • 3d ago #viralvideo #fypage #typシ Viral • Wealth© @Adufe N •Adewealth ARODUN DI 日必 HARDEYJOKEH*! #fffffffffffyyyyYYYyyYypppppppppppp #varilvideo #500kviews #nigerialovecouple #fyppppppppppppppppppppppp #fyp #dariyazallah 之 乏#breketefamily

♬ original sound – Moh___Zyynsanee

A wannan rikicin dai, ra’ayoyin mutane ya banbanta.

Karanta Wannan  Duk da Jhuyin mulkin bai faru ba, ji yanda ministan kudi, Wale Edun ya yanke jiki ya Fhadi sumamme bayan da ya ga sunansa cikin wadanda sojojin da suka Shirya yiwa shugaba Tinubu Jhuyin mulki zasu Shekye

Inda wasu suka goyi bayan bangaren Aminu J. Town wasu kuma suka goyi bayan bangaren Ordinary president da matar soja.

Wasu sun yi zargin cewa Ordinary president ne ya tirsasawa matar sojan kin amincewa da maganar nema mata tallafi da Aminu J. Town yayi, ita kuma ganin tana karkashin gidan talabijin dinsa ne kuma ta nan ne zai nema mata taimako yasa ta amince da duk sharadinsa.

Masu shashi sun ci gaba da cewa Ahmad Isa na kokarin ganin ya yi amfani da wannan magana ta matar soja wajan kara samarwa gidan talabijin dinsa farin jini.

Saidai wasu na ganin Ahmad Isa din ya wuce da haka, Asalima ba sa’an yin Aminu J. Town bane.

Wasu masu sharhin na ganin cewa, maganganun da Aminu J. Town yayi na rashin kunyane ga Ordinary president wanda basu kamata ba saboda ba sa’an yinsa bane.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *