Monday, December 16
Shadow

Matawalle na da hannu a aikin ƴan fashin jeji, in ji Gwamnan Zamfara

Gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya yi zargin cewa magabacinsa, Bello Matawalle, na da hannu dumu-dumu a aiyukan ƴan fashin jeji da suka addabi jihar.

Jaridar PUNCH ta rawaito cewa da ya ke magana a wani shirin siyasa na gidan talabijin na TVC a daren jiya Laraba, gwamnan ya yi ikirarin cewa, bisa bayanan da su ka samu, magabacinsa ya jagoranci gwamnatin da ke hada kai da ƴan fashin jeji su na aikata ta’addanci.

Lawal ya kuma zargi gwamnatin da ta shude a karkashin Bello Matawalle, wanda a yanzu shi ne karamin ministan tsaro da karkatar da kudaden jihar da kuma yin sakaci da harkar tsaro a jihar.

Karanta Wannan  Atiku, Kwankwaso: Dalilan Da Ya Sa Arewa Ba Za ta Iya Magana Da Murya Ɗaya Ba A 2027 – Buba Galadima

“Eh, akwai batutuwa da yawa a baya daga gwamnatin da ta gabata. A gaskiya, bari in fadi wannan sarai: da nine shi (Matawalle) zan yi murabus in fuskanci duk wani zargi da ake min, hakan shi ne mutunci a tare da shi..

“Daga dukkan bayanan da muke samu, magabaci na (Matawalle) na da hannu dumu-dumu a wasu daga cikin wadannan al’amuran na ‘yan fashin jeji” in ji Lawal.

Da ya ke tabbatar da ikirarin da ya yi na cewa magabacinsa na da hannu a ‘yan fashin jeji, ya bayyana yadda wani sakatare na dindindin a gwamnatin Matawalle ya biya kudin fansa ta gidan gwamnati domin a sako ‘ya’yansa da ‘yan bindiga su ka sace,” in ji shi.

Karanta Wannan  Ga masu cewa basu ga dalilin dawo da tsohon taken Najeriya ba, ku sani dawo da taken Najeriyar na daya daga cikin muhimman aikin da nake son yi>>Tinubu

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *