Sunday, January 5
Shadow

Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu zai sallami ministoci 11 da sauran manyan ma’aikata

Rahotanni sun bayyana cewa, shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu zai sallami Ministoci 11 daga majalisarsa ta zartaswa.

Me baiwa shugaban kasa shawara kan harkokin yada labarai,Bayo Onanuga ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar.

Saidai bai fadi zuwa yaushene Shugaban kasar zai dauki wannan mataki ba.

Amma wata majiya a fadar shugaban kasar tace a cikin satin da mukene ake tsammanin za’a fitar da sanarwar garambawul din.

Matsin rayuwa na daya daga cikin abinda ‘yan Najeriya ke kuka dashi a gwamnatin Bola Ahmad Tinubu wanda ke da alaka da yanayin mulkin da yake gudanarwa.

Karanta Wannan  Da Duminsa: Kalli Bidiyo yanda shugaban kasa Bola Ahmad Tinubu ya yi tuntube ya fadi a wajan taron ranar 'yanci

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *