Monday, December 16
Shadow

Wata Sabuwa: Gwamnati ta saka haraji akan gawarwaki a Najeriya

Gwamnatin jihar Enugu ta sanar da saka haraji akan gawarwakin da aka ajiye a mutuwaren dake Asibitocin jihar.

Saidai gwamnatin tace ba da niyyar tatsar mutane da tara kudade barkatai bane ta aikata hakan.

Shugaban hukumar tara kudaden shiga na jihar, Mr Emmanuel Nnamani

Ya yi karin haske kan lamarin inda yace duk gawar da aka kai mutuware a jihar kuma ‘yan uwanta basu dauketa ba har ta wuce awanni 24 watau kwana daya to duk rana za’a rika biya mata harajin Naira 40 har zuwa ranar da za’a dauketa daga mutuwaren.

Yace wannan ba sabuwar haraji bace kuma an dauki matakinne dan hana mutane kai gawarwakinsu mutuware a jihar.

Karanta Wannan  An kama Boka bayan da ya baiwa wani mutum maganin bindiga kuma aka yi gwajin harba bindigar saidai maganin bai yi aiki ba, Mutumin ya mutu

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *