Wani mutum ya mutu yana tsaka da lalata da wata mata a jihar Naija.
Lamarin ya farune a karamar hukumar Paiko dake jihar ranar 15 ga watan October.
Kakakin ‘yansandan jihar, SP Wasi’u Abiodun ya tabbatar da faruwar lamarin inda yace zuwa yanzu ba’a kai ga tantance mutumin ba ko danginsa saboda babu wata shaida ko waya a tare dashi.
Yace mutumin ya shiga otal dinne da wata mata wadda ake kyautata zaton karuwace bayannan ya yanke jiki ya fadi.
Yace an garzaya dashi Asibiti inda likitoci suka tabbatar da ya mutu.