Bankin Duniya ya gargadi gwamnatin shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu da kada ta sake ta dawo da biyan tallafin man fetur inda yace idan aka dawo aka ci gaba da biyan tallafin man fetur din,kasar zata fada bala’i.
Wakilin bankin Duniyar, Dr. Ndiame Diop ne ya bayyana haka a wajan wani taro a Abuja inda yace duk da yake wadannan tsare-tsare na gwamnati na saka mutane cikin wahala amma sune mafita.
Bayan cire tallafin man fetur farashinsa ya tashi daga Naira 198 akan kowace lita zuwa sama da Naira 1000 akan kowace lita.
Hakanan itama dala bayan cire tallafinta ta tashi daga 600 zuwa 1700 akan kowace dala.
‘Yan Najeriya da yawa dai na kokawa akan wannan tsari.
Ministan kudi, Mr. Wale Edunya tabbatar da cewa, Gwamnati zata tsaya tsayin daka akan wadannan tsare-tsare ba zata koma baya ba.